Skip to content
Daniyel 3:3-12

Daniyel 3:3-12

3
Saboda haka sai hakimai, da wakilai da gwamnoni, mashawarta da ma’aji da alƙalai, da marubutan alƙalai, da kuma dukan ma’aikatan yankunan suka tattaru domin kaddamar da siffar da Nebukadnezzar ya kafa, suka kuma tsaya a gabansa.
4
Sai mai shela ya daga murya da ƙarfi ya ce, “Wannan shi ne abin da aka umarce ku ku yi, ya ku mutane da al’umma da kowane yare.
5
Da zarar kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya da goge da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ku rusuna ku yi sujada ga wannan gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa.
6
Duk wanda bai rusuna ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a cikin tendarun wuta.”
7
Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa.
8
A wannan lokaci sai waɗansu masanan taurari suka zo gaba suka yi karar Yahudawa.
9
Suka ce wa sarki Nebukadnezzar, “Ran sarki yă daɗe,
10
Ya sarki, ka fitar da doka, cewa duk wanda ya ji karar ƙaho, da sarewa, da garayu da goge, da molo da algaita da kowane irin kayan kaɗe-kaɗe da bushe-bushe sai yă rusuna yă yi sujada ga siffar zinariya,
11
kuma cewa duk wanda bai rusuna ya yi sujadar ba za a jefa shi cikin tanderun wuta.
12
Amma sai ga waɗansu Yahudawa waɗanda ka ɗora su a kan harkokin yankin Babilon, wato, Shadrak, Meshak da Abednego waɗanda ba su kula da umarninka ba, ya sarki. Ba su bauta wa allolin ba balle su yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options