Skip to content
Daniyel 2:1-9

Daniyel 2:1-9

1
A shekara ta biyu ta mulkinsa, Nebukadnezzar ya yi mafarkai; hankalinsa ya tashi har ya kāsa barci.
2
Sai sarki ya sa aka tattara masa masu sihiri da masu dabo da bokaye da masanan taurari domin su faɗi abin da ya yi mafarki a kai. Da suka shigo suka tsaya a gaban sarki,
3
sai ya ce musu, “Na yi mafarkin da ya dame ni kuma ina so in san me yake nufi.”
4
Sai masanan taurarin suka amsa wa sarki da Arameyanci “Ran sarki yă daɗe! Ka faɗa wa bayinka mafarkin, mu kuma sai mu fassara.”
5
Sai sarki ya amsa wa masanan taurarin ya ce, “Na mance da abin, idan ba ku tuno mini mafarkin, duk da fassararsa ba, to, za a daddatse ku gunduwa-gunduwa, a mai da gidajenku juji.
6
Amma in har kuka faɗa mini mafarkina kuka kuma bayyana fassararsa, za ku sami lada mai girma. Saboda haka ku faɗa mini mafarkin da kuma fassararsa.”
7
Sai suka sāke amsa masa suka ce, “Ran sarki yă daɗe, faɗa wa bayinka mafarkin, mu kuma za mu fassara shi.”
8
Sai sarki ya amsa ya ce, “Na gane cewa kuna ƙoƙari ku ɓata lokaci ne kawai domin ku ga na manta da abin.
9
In ba ku faɗa mini mafarkin ba, akwai hukunci guda ɗaya kurum dominku. Kun haɗa baki domin ku faɗa mini munanan al’amura domin ku ruɗe ni har lokaci yă wuce. Sai ku faɗa mini mafarkin, ta haka kuwa zan sani za ku iya yi mini fassararsa.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options