Skip to content
Amos 9:1-6

Amos 9:1-6

1
Na ga Ubangiji yana tsaye a gaban bagade, ya kuma ce, “Bugi kan ginshiƙan don madogaran ƙofa su girgiza. Saukar da su a kan dukan mutane; waɗanda ba su mutu ba zan kashe su da takobi. Ba mutum guda da zai tsere, babu wani da zai tsira.
2
Ko da sun tona rami kamar zurfin kabari, daga can hannuna zai fitar da su. Ko da sun hau can sama daga can zan sauko da su.
3
Ko da sun ɓuya a bisa Karmel, a can zan farauce su in cafko. Ko da sun ɓuya can ƙarƙashin teku, a can zan umarci maciji yă sare su.
4
Ko da abokan gābansu sun kore su zuwa zaman bauta, a can zan umarci takobi yă kashe su. “Zan sa musu ido don mugunta ba don alheri ba.”
5
Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, shi da yakan taɓa ƙasa sai ta narke, kuma dukan mazauna cikinta suna makoki, ƙasar gaba ɗaya takan hau ta kuma sauka kamar Nilu, sa’an nan ta nutse kamar kogin Masar,
6
shi da ya gina kyakkyawar fadarsa a cikin sammai ya kuma kafa harsashenta a duniya, shi da yakan kira ruwan teku yă kuma kwarara su a bisa duniya, Ubangiji ne sunansa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options