Skip to content
Amos 7:14-17

Amos 7:14-17

14
Amos ya amsa wa Amaziya, “Ni ba annabi ba ne ko ɗan annabi, amma ni makiyayi ne, kuma ina lura da itatuwan al’ul.
15
Amma Ubangiji ya ɗauke ni daga kiwon dabbobi ya ce mini, ‘Je ka, ka yi wa mutanena Isra’ila annabci.’
16
Yanzu fa, sai ka ji maganar Ubangiji. Ka ce, “ ‘Kada in yi annabci a kan Isra’ila, kuma in daina yin wa’azi a kan gidan Ishaku.’
17
“Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “ ‘Matarka za tă zama karuwa a cikin birni, kuma da takobi za a kashe ’ya’yanka maza da mata. Za a auna ƙasarka a kuma raba ta, kai kuma za ka mutu a ƙasar arna. Ba shakka Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options