Amos 7:10-13
10
Sai Amaziya firist na Betel ya aika da saƙo zuwa wurin Yerobowam sarkin Isra’ila. “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a tsakiyar Isra’ila. Ƙasar ba za tă iya ɗauka abubuwan da yake faɗi ba.
11
Gama ga abin da Amos yake cewa, “ ‘Yerobowam zai mutu ta wurin takobi, kuma tabbatacce Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”
12
Sai Amaziya ya ce wa Amos, “Tafi daga nan, mai duba kawai! Koma ƙasar Yahuda. Ka nemi abin zaman garinka a can ka kuma yi annabcinka a can.
13
Kada ka ƙara yin annabci a Betel, gama nan wuri mai tsarki ne na sarki da kuma haikalin ƙasar.”
Settings