Skip to content
Ayyukan Manzanni 8:18-24

Ayyukan Manzanni 8:18-24

18
Sa’ad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi,
19
ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yă karɓi Ruhu Mai Tsarki.”
20
Bitrus ya amsa ya ce, “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi!
21
Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba.
22
Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka.
23
Gama na lura kana cike da ɗacin rai kana kuma daure cikin zunubi.”
24
Sai Siman ya amsa ya ce, “Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda ni don kada ko ɗaya daga cikin abin da ka faɗa ya same ni.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options