Ayyukan Manzanni 7:54-60
54
Da membobin Sanhedrin suka ji haka, sai suka yi fushi suka ciji haƙoransu.
55
Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah.
56
Ya ce, “Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah.”
57
Da jin haka sai suka tattoshe kunnuwansu, suka kuma yi ihu da ƙarfi sosai, suka aukar masa gaba ɗaya.
58
Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu.
59
Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi addu’a ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.”
60
Sa’an nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci.
Settings