Ayyukan Manzanni 6:3-8
3
’Yan’uwa, ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku waɗanda aka sani suna cike da Ruhu da kuma hikima. Mu kuwa za mu danƙa musu wannan aiki
4
mu kuwa mu mai da halinmu ga yin addu’a da kuma hidimar maganar Allah.”
5
Wannan shawarar kuwa ta gamshi dukan ƙungiyar. Sai suka zaɓi Istifanus, mutumin da yake cike da bangaskiya da kuma Ruhu Mai Tsarki; da Filibus, Burokorus, Nikano, Timon, Farmenas, da Nikolas daga Antiyok, wanda ya tuba zuwa Yahudanci.
6
Suka gabatar da waɗannan mutane wa manzanni, waɗanda kuwa suka yi addu’a, suka ɗibiya hannuwansu a kansu.
7
Saboda haka maganar Allah ta yaɗu. Yawan almajirai a Urushalima kuwa ya yi saurin ƙaruwa, firistoci masu yawa kuma suka zama masu biyayya ga wannan bangaskiya.
8
To, Istifanus, mutum cike da alheri da ikon Allah, ya aikata manyan ayyukan da alamu masu banmamaki a cikin mutane.
Settings