Ayyukan Manzanni 5:29-42
29
Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce, “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane!
30
Allahn kakanninmu ya tā da Yesu daga matattu, wanda kuka kashe ta wurin ratayewa a bisan itace.
31
Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don yă kawo tuba da gafarar zunubai ga Isra’ila.
32
Mu shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya ba wa waɗanda suke yin masa biyayya.”
33
Da suka ji haka, sai suka yi fushi suka so su kashe su.
34
Amma wani Bafarisiyen da ake kira Gamaliyel, wani malamin doka, wanda dukan mutane ke girmamawa, ya miƙe tsaye a Majalisar ya umarta a fitar da mutanen waje na ɗan lokaci.
35
Sa’an nan ya yi musu jawabi ya ce, “Mutanen Isra’ila, ku yi kula da kyau da abin da kuke niyyar yi wa mutanen nan.
36
Kwanan baya, Teyudas ya ɓullo, yana cewa wai shi wani mutum ne, kuma wajen mutane ɗari huɗu suka bi shi. Aka kuwa kashe shi, dukan masu binsa kuwa suka watse, kome ya wargaje.
37
Bayansa, Yahuda mutumin Galili ya ɓullo a kwanakin ƙidaya, ya jagoranci mutane cikin tawaye. Shi ma aka kashe shi, dukan mabiyansa kuma aka watsar da su.
38
Saboda haka, a wannan batu na yanzu, ina ba ku shawara. Ku ƙyale mutanen nan! Ku bar su su tafi! Gama in manufarsu ko ayyukansu na mutum ne, ai, zai rushe.
39
Amma in daga Allah ne, ba za ku iya hana waɗannan mutane ba, za ku dai sami kanku kuna gāba da Allah ne.”
40
Jawabinsa ya rinjaye su. Suka kira manzannin suka sa aka yi musu bulala. Sa’an nan suka kwaɓe su kada su ƙara magana a cikin sunan Yesu, suka kuma bar su suka tafi.
41
Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan.
42
Kowace rana, a filin haikali da kuma gida-gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba.
Settings