Ayyukan Manzanni 27:41-44
41
Amma jirgin ruwan ya shiga yashi ya kafe. Kan jirgin ya shiga cikin yashin ya kāsa motsi, sai jirgin ya fara farfashewa ta baya saboda haukan raƙuman ruwa.
42
Sojojin suka yi niyya su kakkashe ’yan kurkukun don hana waninsu yă yi iyo yă tsere.
43
Amma jarumin ya so yă ceci ran Bulus, sai ya hana su aiwatar da niyyarsu. Ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci.
44
Sauran kuma su bi katakai zuwa can ko kuma a kan tarkacen jirgin ruwan. Ta haka kowa ya kai bakin teku lafiya.
Settings