Ayyukan Manzanni 25:6-12
6
Bayan ya yi kwanaki takwas ko goma tare da su, sai ya gangara zuwa Kaisariya, kashegari kuma ya kira a yi zaman kotu ya kuma umarta a kawo Bulus a gabansa.
7
Da Bulus ya bayyana, sai Yahudawan da suka gangaro daga Urushalima suka tsaya kewaye shi, suna kawo ƙarar masu tsanani da yawa a kansa, waɗanda ba su iya tabbatarwa ba.
8
Sa’an nan Bulus ya kāre kansa ya ce, “Ban aikata wani laifi game da dokokin Yahudawa ko game da haikali ko kuma game da Kaisar ba.”
9
Festus, da yake yana so yă yi wa Yahudawa alfarma, sai ya ce wa Bulus, “Ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari’a a can a gabana a kan waɗannan zarge?”
10
Bulus ya amsa ya ce, “Yanzu ina tsaye a gaban kotun Kaisar, inda ya kamata a yi mini shari’a. Ban yi wani laifi ga Yahudawa ba, kai da kanka ma ka san da haka sarai.
11
In kuwa ina da wani laifin da ya isa kisa, ban ƙi in mutu ba. Amma in ƙarar da waɗannan Yahudawa suka kawo a kaina ba gaskiya ba ne, ba wanda yake da iko ya ba da ni a gare su. Na ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar!”
12
Bayan Festus ya yi shawara da majalisarsa sai ya ce, “Ka ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar. To, ga Kaisar kuwa za ka tafi!”
Settings