Skip to content
Ayyukan Manzanni 20:7-12

Ayyukan Manzanni 20:7-12

7
A ranar farko ta mako muka taru wuri ɗaya don gutsuttsura burodi. Bulus ya yi wa mutane magana, don yana niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta yin magana har tsakar dare.
8
Akwai fitilu da yawa a ɗakin gidan saman da muka taru.
9
Akwai wani saurayi zaune a taga mai suna Yitikus, wanda barci mai nauyi ya ɗauke shi yayinda Bulus yake ta tsawaita magana. Sa’ad da yake barci, sai ya fāɗi daga gidan sama a hawa ta uku aka kuma ɗauke shi matacce.
10
Sai Bulus ya sauka, ya miƙe a kan saurayin ya rungume shi ya ce, “Kada ku damu, yana da rai!”
11
Sai ya koma ɗakin da yake a gidan sama, ya gutsuttsura burodi ya kuma ci. Bayan ya yi magana har gari ya waye, sai ya tafi.
12
Mutanen suka ɗauki saurayin da rai zuwa gida suka kuma ta’azantu ƙwarai da gaske.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options