Skip to content
Ayyukan Manzanni 13:23-39

Ayyukan Manzanni 13:23-39

23
“Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Isra’ila Mai Ceto Yesu, kamar yadda ya yi alkawari.
24
Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi wa’azin tuba da baftisma ga dukan mutanen Isra’ila.
25
Yayinda Yohanna yake kammala aikinsa ya ce, ‘Wa kuke tsammani ni nake? Ba ni ne shi ba. A’a, amma yana zuwa bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in kunce ba.’
26
“Ya ku ’yan’uwa, ’ya’yan Ibrahim, da ku kuma Al’ummai masu tsoron Allah, a gare mu ne fa aka aiko wannan saƙon ceto.
27
Mutanen Urushalima da masu mulkinsu ba su gane da Yesu ba, duk da haka cikin hukunta shi suka cika kalmomin annabawan da ake karantawa kowane Asabbaci.
28
Ko da yake ba su same shi da wani dalilin da ya kai ga hukuncin kisa ba, suka roƙi Bilatus yă sa a kashe shi.
29
Sa’ad da suka aikata duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka saukar da shi daga itacen suka kuma sa shi a kabari.
30
Amma Allah ya tashe shi daga matattu,
31
kuma kwanaki da yawa waɗanda suka yi tafiya tare da shi daga Galili zuwa Urushalima suka gan shi. Su ne yanzu shaidu ga mutanenmu.
32
“Muna gaya muku labari mai daɗi cewa abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari,
33
ya cika mana, mu zuriyarsu, ta wurin tā da Yesu daga matattu. Kamar yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa, “ ‘Kai Ɗana ne, yau na zama Uba a gare ka.’
34
Gaskiyar cewa Allah ya tā da shi daga matattu, a kan ba zai taɓa ruɓewa ba, an faɗe shi a cikin waɗannan kalmomi. “ ‘Zan ba ku tsarki da kuma tabbatattun albarkun da na yi wa Dawuda alkawari.’
35
Haka kuma aka faɗa a wani wuri. “ ‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’
36
“Gama sa’ad da Dawuda ya gama hidimar nufin Allah a zamaninsa, sai ya yi barci; aka binne shi tare da kakanninsa jikinsa kuwa ya ruɓe.
37
Amma wanda Allah ya tā da daga matattu bai ruɓa ba.
38
“Saboda haka, ’yan’uwana, ina so ku san cewa ta wurin Yesu ana sanar muku da gafarar zunubi.
39
Ta wurinsa kowa da ya gaskata an kuɓutar da shi daga dukan abin da Dokar Musa ba tă iya kuɓutar ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options