Ayyukan Manzanni 12:12-19
12
Da ya gane haka, sai ya tafi gidan Maryamu uwar Yohanna, wanda ake kuma kira Markus, inda mutane da yawa suka taru suna addu’a.
13
Bitrus ya ƙwanƙwasa ƙofar waje, sai wata mai aiki a gidan da ake kira Roda ta zo tă ji ko wane ne.
14
Da ta gane muryar Bitrus, ta cika da murna ta gudu ta koma ba tare da ta buɗe ƙofar ba, sai ta koma a guje ta ce da ƙarfi, “Ga Bitrus a bakin ƙofa!”
15
Sai suka ce mata, “Kina hauka.” Da ta nace cewa shi ne, sai suka ce, “To, lalle, mala’ikansa ne.”
16
Amma Bitrus ya yi ta ƙwanƙwasawa. Da suka buɗe ƙofar suka kuma gan shi, sai suka yi mamaki.
17
Bitrus ya yi musu alama da hannunsa su yi shiru sai ya bayyana yadda Ubangiji ya fitar da shi daga kurkuku. Ya ce, “Ku gaya wa Yaƙub da kuma ’yan’uwa game da wannan,” sa’an nan ya tashi ya tafi wani wuri.
18
Da safe, hargitsin da ya tashi tsakanin sojojin ba ƙarami ba ne, a kan abin da ya sami Bitrus.
19
Bayan Hiridus ya neme shi bai same shi ba, sai ya tuhumi masu gadin, ya kuma ba da umarni a kashe su. Sa’an nan Hiridus ya tashi daga Yahudiya ya tafi Kaisariya ya kuma yi ’yan kwanaki a can.
Settings