Ayyukan Manzanni 12:1-4
1
Kusan a wannan lokaci ne Sarki Hiridus ya kama waɗansu da suke na ikkilisiya, da niyya ya tsananta musu.
2
Ya sa aka kashe Yaƙub, ɗan’uwan Yohanna, da takobi.
3
Sa’ad da ya ga wannan ya faranta wa Yahudawa rai, sai ya kama Bitrus shi ma. Wannan ya faru kwanakin Bikin Burodi Marar Yisti.
4
Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shari’a a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa.
Settings