Ayyukan Manzanni 11:19-21
19
To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin da ya tashi a kan batun Istifanus suka tafi har Funisiya, Saifurus da kuma Antiyok, suna ba da saƙon ga Yahudawa kaɗai.
20
Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Hellenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu.
21
Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji.
Settings