Skip to content
Ayyukan Manzanni 10:1-4

Ayyukan Manzanni 10:1-4

1
A Kaisariya akwai wani mutum mai suna Korneliyus, wani jarumin Roma ne, a ƙungiyar soja da ake kira Bataliyar Italiya.
2
Shi da dukan iyalinsa masu ibada ne masu tsoron Allah kuma; yakan ba da kyauta hannu sake ga masu bukata yana kuma addu’a ga Allah ba fasawa.
3
Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani mala’ikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!”
4
Korneliyus kuwa ya zura masa ido a tsorace ya ce, “Mene ne, ya Ubangiji?” Mala’ikan ya ce, “Addu’o’inka da kyautanka ga matalauta sun kai har sama, hadayar tunawa ce a gaban Allah.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options