2 Timoti 1:2-4
2
Zuwa ga Timoti, ƙaunataccen ɗana. Alheri, jinƙai da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.
3
Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina.
4
Sa’ad da na tuna da hawayenka, nakan yi marmarin ganinka, don in cika da farin ciki.
Settings