Skip to content
2 Sama’ila 8:1-8

2 Sama’ila 8:1-8

1
Ana nan, sai Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi, ya kawo ƙarshen mulkinsu a ƙasar, ya kuma ƙwace ƙasar Meteg Amma daga hannun Filistiyawa.
2
Haka kuma Dawuda ya ci Mowabawa. Ya sa suka kwanta a ƙasa, ya kuma auna su da igiya. Kowane awo biyu ya sa a kashe su, amma awo na uku sai yă sa a bar su da rai. Saboda haka Mowabawa suka zama bayin Dawuda, suka kuma kawo masa haraji.
3
Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba. Wannan ya faru a lokacin da Hadadezer yake kan hanyarsa zuwa Kogin Yuferites don yă sāke mai da wurin a ƙarƙashin ikonsa.
4
Dawuda ya kame keken yaƙinsa guda dubu, mahayan keken yaƙinsa dubu bakwai, da sojojin ƙasa dubu ashirin. Ya yayyanke agaran dawakan duka amma ya bar dawakai kekunan yaƙi ɗari.
5
Sa’ad da Arameyawan Damaskus suka zo don su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya karkashe dubu ashirin da biyunsu.
6
Ya ajiye ƙungiyoyi sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus, Arameyawa kuwa suka zama bayinsa, suka biya shi haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a duk inda ya tafi.
7
Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariya na shugabannin sojojin Hadadezer ya kawo Urushalima.
8
Daga Teba da Berotai, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Sarki Dawuda ya kwashe tagulla masu yawan gaske.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options