1
Dawuda ya sāke tattara zaɓaɓɓun mutanen Isra’ila, dubu talatin.
2
Shi, da dukan mutanensa suka tashi daga Ba’ala-Yahuda don su hauro da akwatin alkawarin Allah, wanda ake kira da Sunan Ubangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a tsakanin kerubobin da suke a kan akwatin alkawarin.