Skip to content
2 Sama’ila 16:1-4

2 Sama’ila 16:1-4

1
Sa’ad da Dawuda ya yi ɗan nesa da ƙwanƙolin, sai ga Ziba mai hidimar Mefiboshet, yana jira yă tarye shi. Yana da jerin jakuna da sirdi suna ɗauke da dunƙulen burodi ɗari biyu, da ƙosai busasshen inabi ɗari ɗaya, da kosan ’ya’yan itace ɓaure guda ɗari, da salka ruwan inabi.
2
Sarki ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo waɗannan?” Ziba ya ce, “Jakuna domin iyalin gidan sarki su hau ne, burodi da ’ya’yan itace domin mutane su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suka gaji a hamada.”
3
Sai sarki ya ce, “Ina jikar maigidanka?” Ziba ya ce, “Yana zaune a Urushalima gama yana tsammani cewa, ‘Yau gidan Isra’ila za su mayar mini da sarautar kakana.’ ”
4
Sai sarki ya ce wa Ziba, “Duk abin da yake na Mefiboshet, ya zama naka.” Ziba ya rusuna ya ce, “Bari in dinga samun tagomashi a gabanka ranka yă daɗe.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options