2 Sama’ila 10:18-19
18
Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, Dawuda kuwa ya kashe mahayan keken yaƙinsu ɗari bakwai, da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya bugi Shobak, shugaban ƙungiyar sojansu ya kuwa mutu a can.
19
Sa’ad da dukan sarakuna waɗanda suke abokan tarayya na Hadadezer suka ga Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka yi sulhu da Isra’ilawa, suka kuma zama bayinsu. Wannan ya sa Arameyawa suka ji tsoron ƙara kai wa Ammonawa gudummawa.
Settings