2 Sarakuna 9:21-24
21
Yoram ya umarta, “Haɗa mini keken yaƙi!” Da aka haɗa, sai Yoram sarkin Isra’ila, da Ahaziya sarkin Yahuda, suka hau suka tafi, kowa a keken yaƙinsa, don su taryi Yehu. Suka sadu da shi a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel.
22
Sa’ad da Yoram ya ga Yehu sai ya tambaye shi, “Lafiya kuwa ka zo, Yehu?” Yehu ya ce, “Ina kuwa lafiya, da yake dukan bautar gumaka da bokancin mahaifiyarka Yezebel sun bazu ko’ina?”
23
Yoram ya juya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya, “Cin amana, Ahaziya!”
24
Sai Yehu ya ja bakansa ya harbi Yoram a tsakanin kafaɗunsa. Kibiyar ta same shi a zuciyarsa sai ya fāɗi a cikin keken yaƙinsa.
Settings