2 Sarakuna 8:18
Ana nuna aya 18 tare da mahallin da ke kewaye.
15
Amma kashegari sai ya ɗauki tsumma mai kauri, ya jiƙa shi, ya rufe fuskar sarki da shi, har sai da sarki ya mutu. Sai Hazayel ya gāje shi a matsayin sarki.
16
A shekara ta biyar ta mulkin Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra’ila, sa’ad da Yehoshafat yake sarautar Yahuda, Yoram ɗan Yehoshafat, ya fara mulkinsa a matsayin sarkin Yahuda.
17
Yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki na tsawon shekara takwas a Urushalima.
18
Ya bi gurbin sarakunan Isra’ila, yadda gidan Ahab ta yi, gama ya auri ’yar Ahab. Ya yi mugunta a gaban Ubangiji.
19
Duk da haka, saboda bawansa Dawuda, Ubangiji bai ragargaza Yahuda ba. Ya riga ya yi alkawari zai bar wa Dawuda magāji har abada.
20
A kwanakin Yoram, Edom ta yi wa Yahuda tawaye, ta naɗa wa kanta sarki.
21
Saboda haka Yehoram ya tafi Zayir da dukan kekunan yaƙinsa. Sojojin Edom suka kewaye shi a can, amma da dare sai Yoram ya ɓarke ya gudu, sojojinsa kuma suka watse zuwa gidajensu.
Settings