2 Sarakuna 7:8-11
8
Da kutaren nan suka kai bakin sansanin, sai suka shiga wani tenti, suka ci, suka sha, suka kwashi azurfa, da zinariya, da riguna, suka tafi, suka ɓoye su. Sa’an nan suka koma, suka shiga wani tenti, sai suka kwashi kaya daga ciki, suka kuma ɓoye su.
9
Sa’an nan suka ce wa juna, “Ba mu yi abin kirki ba. Wannan rana ce ta albishiri amma muka yi shiru; in kuwa mun bari har gari ya waye, to, fa, wata masifa za tă fāɗo mana. Bari mu tafi nan take mu faɗa a fadan sarki.”
10
Saboda haka suka je suka kira masu tsaron ƙofar birni, suka ce musu, “Mun je sansanin Arameyawa, ga shi kuwa ba mu iske kowa a can ba, babu ko motsin wani, sai dai dawakai da jakuna a daure, tentunan kuwa suna nan yadda suke.”
11
Sai matsaran ƙofar suka sanar da labarin a cikin fada.
Settings