Skip to content
2 Sarakuna 6:24-33

2 Sarakuna 6:24-33

24
Bayan wani lokaci, Ben-Hadad sarkin Aram ya tattara dukan rundunarsa, ya je ya kewaye Samariya da yaƙi.
25
Aka yi babban yunwa a cikin birnin. Saboda daɗewar wannan kewayewar da aka yi wa birnin, sai yunwa ta ɓarke a birnin, har ana sayar da kan jaki a kan shekel tamanin, kashin kurciya kuma a kan shekel biyar.
26
Yayinda sarkin Isra’ila yake wucewa kusa da katanga, sai wata mace ta yi masa kuka ta ce, “Ka taimake ni, ranka yă daɗe, sarki!”
27
Sai sarki ya amsa ya ce, “In Ubangiji bai taimake ki ba, me zan iya yi? Ina da hatsi ko ruwan inabin da zan ba ki ne?”
28
Sa’an nan ya tambaye ta ya ce, “Me ya faru?” Sai ta amsa ta ce, “Wannan mace ta ce mini, ‘Kawo ɗanki mu ci yau, gobe kuwa mu ci ɗana.’
29
Saboda haka muka dafa ɗana muka ci. Kashegari na ce mata, ‘Kawo ɗanki mu ci,’ amma ta ɓoye shi.”
30
Da sarki ya ji maganar macen sai ya yage rigunansa. Sa’ad da sarki yake wucewa a kan katangar birnin, sai mutane suka gan yana saye da rigar makoki a ciki.
31
Ya ce, “Bari Allah yă yi mini hukunci mai tsanani har ma fiye da haka, idan ban cire kan Elisha ɗan Shafat yau ba!”
32
To, Elisha yana zaune a cikin gidansa, dattawa kuwa suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki ɗan aika yă ci gaba, amma kafin ɗan aikan yă isa, Elisha ya ce wa dattawan, “Kun gani ko? Wannan mai kisa ya aiko a cire mini kai! To, idan ɗan aikan ya iso, sai ku rufe ƙofar da ƙarfi, ku bar shi a waje. Ba da jimawa ba, maigidansa zai bi bayansa?”
33
Yana magana da su ke nan, sai ga ɗan aikan ya gangaro wajensa. Sarki kuma ya ce, “Wannan bala’in daga wurin Ubangiji ya fito. Don me zan sa zuciya ga Ubangiji kuma?”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options