2 Sarakuna 3:20-25
20
Kashegari, daidai lokacin hadaya, sai ga ruwa yana gangarowa daga gefen Edom! Ƙasar kuwa ta cika da ruwa.
21
To, dukan Mowabawa suka ji cewa sarakuna suna tafe don su yaƙe su; saboda haka aka kira kowane namiji, babba da yaro, wanda ya isa ɗaukan makami, aka jera su a bakin iyaka.
22
Da suka tashi da sassafe, rana tana haska ruwa. Sai ruwan ya yi ja kamar jini a idanun Mowabawan da suke a ƙetare.
23
Sai suka ce, “Jini ne! Ba shakka sarakunan nan sun yaƙe juna, suka karkashe juna. Ya Mowabawa, mu tafi mu kwashi ganima!”
24
Amma da Mowabawa suka isa sansanin Isra’ila, sai Isra’ilawa suka taso suka auka musu har sai da suka gudu. Isra’ilawa kuwa suka kai musu hari, suka karkashe Mowabawa.
25
Suka ragargaza garuruwa, kowane mutum kuwa ya jefa dutse a kowane gona mai kyau har sai da aka rufe gonakin gaba ɗaya. Suka tattoshe duk maɓulɓulan ruwa, suka kuma sare duk itace mai kyau. Kir Hareset ne kaɗai aka bari tare da duwatsunsa yadda suke, amma mutanen da suke da majajjawa suka yi wa birnin zobe, suka kai masa hari shi ma.
Settings