2 Sarakuna 13:15-18
15
Elisha ya ce wa Yehowash, “Ka samo baka da kibiyoyi,” ya kuwa yi haka.
16
Sai ya ce wa Yehowash sarkin Isra’ila, “Ka ɗauki baka a hannunka.” Da ya ɗauka, sai Elisha ya sa hannunsa a hannuwan sarki.
17
Ya ce masa, “Ka buɗe taga wajen gabas,” sai ya buɗe. Sai Elisha ya ce, “Ka harba!” Sai ya harba. Elisha ya ce, “Kibiyar nasara ta Ubangiji, kibiyar nasara a kan Aram! Za ka hallaka Arameyawa sarai a Afek.”
18
Sa’an nan ya ce, “Ka ɗauki kibiyoyi,” sai sarkin ya ɗauko. Sai Elisha ya ce, “Ka caki ƙasa.” Sai ya caka sau uku sa’an nan ya daina.
Settings