2 Sarakuna 13:1-7
1
A shekara ta ashirin da uku ta Yowash ɗan Ahaziya, sarkin Yahuda, Yehoyahaz ɗan Yehu, ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuwa yi mulki shekaru goma sha bakwai.
2
Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji ta wurin bin zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata, bai kuwa guje musu ba.
3
Saboda haka fushin Ubangiji ya ƙuna a kan Isra’ila, kuma da daɗewa ya sa su a ƙarƙashin ikon Hazayel sarkin Aram da Ben-Hadad ɗansa.
4
Sai Yehoyahaz ya nemi tagomashin Ubangiji, Ubangiji kuwa ya saurare shi, domin ya gan irin matsin da sarkin Aram yake yi wa Isra’ila.
5
Sai Ubangiji ya tā da mai ceto wa Isra’ila, suka kuma kuɓuta daga ikon Aram. Ta haka Isra’ilawa suka yi zama a gidajensu yadda suka yi a dā.
6
Sai dai ba su bar yin zunuban gidan Yerobowam ba, wanda ya sa Isra’ila ta aikata; suka ci gaba da yinsu. Haka ma, ginshiƙin Ashera ta kasance a tsaye a cikin Samariya.
7
Ba abin da ya rage na rundunar Yehoyahaz sai mahayan dawakai hamsin, kekunan yaƙi goma da kuma sojoji ƙasa dubu goma. Gama sarkin Aram ya hallaka sauran, ya kuma yi kaca-kaca da su kamar ƙura a masussuka.
Settings