2 Sarakuna 10:1-7
1
To, akwai ’ya’ya maza saba’in na gidan Ahab a Samariya. Saboda haka Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika su Samariya, zuwa ga shugabannin Yezireyel, da kuma ga masu lura da ’ya’yan Ahab. Ya ce,
2
“Da zarar wasiƙan nan ta sadu da ku, da yake ’ya’yan maigidanku suna tare da ku, kuna kuma da kekunan yaƙi da dawakai, da birni mai katanga da makamai,
3
sai ku zaɓi mafi cancanta a cikin ’ya’yan maigidanku ku sa shi a kan kursiyin mahaifinsa. Sa’an nan ku yi yaƙi don gidan maigidanku.”
4
Amma suka razana suka ce, “Idan sarakuna biyu ba su iya yin tsayayya da shi ba, wane mu?”
5
Saboda haka sarkin fada, da gwamnan birnin, da dattawa, da kuma masu lura da ’ya’yan suka aika da saƙo ga Yehu, cewa, “Mu bayinka ne, za mu kuma yi duk abin da ka ce. Ba za mu naɗa kowa sarki ba; sai ka yi abin da ka ga ya fi kyau.”
6
Sai Yehu ya sāke rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “In a gefena kuke, to, sai ku yi biyayya da ni, ku fille kawunan ’ya’yan maigidanku, ku kawo mini a Yezireyel war haka gobe.” To, ’ya’yan sarki, su saba’in, suna tare da manyan birni waɗanda suke lura da su.
7
Sa’ad da wasiƙar ta iso, sai mutanen nan suka ɗauki dukan ’ya’yan sarkin nan saba’in, suka kashe su, suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezireyel.
Settings