2 Korintiyawa 2:7-11
7
Yanzu fa, a maimako, gara ku yafe masa, ku kuma ta’azantar da shi, don kada baƙin ciki mai yawa yă sha kansa.
8
Saboda haka, ina roƙonku, ku sāke nuna masa ƙaunarku.
9
Abin da ya sa na rubuta muku shi ne don in ga ko za ku jimre da gwajin nan, kuna kuma yin biyayya ta kowace hanya.
10
In kuka gafarta wa wani, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta kuwa, in har ma da abin gafartawa, saboda ku ne na gafarta masa, albarkacin Kiristi,
11
don kada Shaiɗan yă rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa.
Settings