2 Tarihi 6:4-15
4
Sa’an nan ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda da hannuwansa ya cika abin da ya yi alkawari da bakinsa ga mahaifina Dawuda. Gama ya ce,
5
‘Tun ranar na da fitar da mutanena daga Masar, ban zaɓi wani birni a wata kabilar Isra’ila don a gina haikali domin Sunana ya kasance a can ba, ba kuwa zaɓi wani yă zama shugaba a bisa jama’ata Isra’ila ba.
6
Amma yanzu na zaɓi Urushalima domin Sunana yă kasance a can, na kuma zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’
7
“Mahaifina Dawuda ya yi niyya a zuciyarsa yă gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.
8
Amma Ubangiji ya ce wa mahaifina Dawuda, ‘Domin yana a zuciyarka ka gina haikali domin Sunana, ka yi daidai da ka kasance da wannan a zuciyarka.
9
Duk da haka, ba kai ba ne za ka gina haikalin, amma ɗanka wanda yake namanka da jininka, shi ne wanda zai gina haikali domin Sunana.’
10
“Ubangiji ya kiyaye alkawarin da ya yi. Na gāje Dawuda mahaifina yanzu kuwa na zauna a kan kujerar sarautar Isra’ila, kamar dai yadda Ubangiji ya alkawarta, na kuma gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.
11
A can na ajiye akwatin alkawari, inda alkawarin Ubangiji da ya yi da mutanen Isra’ila yake.”
12
Sa’an nan Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron Isra’ila ya ɗaga hannuwansa sama.
13
Dā ma ya riga ya gina dakalin tagulla, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kamu biyar da kuma tsayi kamu uku, ya kuma sa shi a tsakiyar filin waje. Ya tsaya a kan dakalin ya kuma durƙusa a gaban dukan taron Isra’ila ya buɗe hannuwansa sama.
14
Ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama da kuma ƙasa, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna tare da bayinka waɗanda suke cin gaba da zuciya ɗaya a hanyarka.
15
Ka kiyaye alkawarinka ga bawanka Dawuda mahaifina; da bakinka ka yi alkawari kuma da hannunka ka cika shi, yadda yake a yau.
Settings