2 Tarihi 6:22-31
22
“Sa’ad da mutum ya yi wa maƙwabcinsa laifi aka kuma bukaci ya yi rantsuwa, ya kuma zo ya rantse a gaban bagadenka a cikin wannan haikali,
23
sai ka ji daga sama ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, kana sāka wa mai laifi ta wurin kawo a kansa hakkin abin da ya yi. Ka nuna cewa marar laifi ba shi da laifi, ta haka a fiffita rashin laifinsa.
24
“Sa’ad da an ci mutanenka Isra’ila a yaƙi ta wurin abokin gāba domin sun yi maka zunubi kuma sa’ad da suka juya suka furta sunanka, suna addu’a suka kuma yin roƙe-roƙe a gabanka a wannan haikali,
25
sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin mutanenka Isra’ila ka kuma dawo da su zuwa ƙasar da ka ba su da kuma kakanninsu.
26
“Sa’ad da sammai suka rufu ba kuwa ruwan sama saboda mutanenka sun yi maka zunubi, sa’ad da kuwa suka yi addu’a suna duban waje wannan wuri suka kuma furta sunanka suka juye daga zunubinsu domin ka azabta su,
27
sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace da za su yi zama, ka kuma aika ruwan sama a ƙasar da ka ba mutanenka gādo.
28
“Sa’ad da yunwa ko annoba ta fāɗo a ƙasar, ko wahala ko fumfuna, ko fāra ko fāra ɗango, ko sa’ad da abokan gāba sun yi musu ƙawanya a kowane daga biranensu, dukan wata masifa ko cutar da za tă zo,
29
sa’ad da kuwa wani cikin mutanenka Isra’ila ya yi wata addu’a ko roƙo, kowa yana sane a azabarsa da kuma zafinsa, yana buɗe hannuwansa yana duban wajen wannan haikali,
30
sai ka ji daga sama, mazauninka. Ka gafarta, ka kuma yi da kowane mutum gwargwadon duk abin da yake yi, da yake ka san zuciyarsa (gama kai kaɗai ka san zukatan mutane),
31
don su ji tsoronka su kuma yi tafiya a hanyoyinka a kowane lokacin da suke zama a ƙasar da ka ba wa kakanninsu.
Settings