2 Tarihi 21:16-20
16
Ubangiji ya sa Filistiyawa da Larabawa waɗanda suke zama kusa da Kushawa su yi gāba da Yehoram
17
Suka yaƙi Yahuda, suka kai masa hari, suka kwashe dukan abubuwa masu kyau da suka samu a fadan sarki, tare da ’ya’yansa maza da kuma matansa. Ba wanda aka bari, sai dai Ahaziya autansa.
18
Bayan dukan wannan, sai Ubangiji ya sa wa Yehoram cuta marar warkarwa ta ciki.
19
Cikin lokaci, a ƙarshen shekara ta biyu, sai hanjin cikinsa suka fito saboda cutar, ya kuma mutu cikin tsananin zafi. Mutanensa suka hura wuta don girmama shi, kamar yadda suka yi wa kakanninsa.
20
Yehoram yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara takwas. Ya mutu, ba ma wanda ya kula, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda, amma ba a makabartan sarakuna ba.
Settings