Skip to content
2 Tarihi 21:12-15

2 Tarihi 21:12-15

12
Yehoram ya sami wasiƙa daga Iliya annabi, wadda ta ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda ya ce, ‘Ba ka yi tafiya a hanyoyin mahaifinka Yehoshafat ko Asa sarkin Yahuda ba.
13
Amma ka yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, ka sa Yahuda ya kauce, ka kuma sa mutanen Urushalima suka yi karuwanci, kamar yadda gidan Ahab ta yi. Ka kuma kashe ’yan’uwanka, membobi gidan mahaifinka, mutanen da suka fi ka kirki.
14
Saboda haka a yanzu Ubangiji yana shirin ya bugi mutanenka, ’ya’yanka maza, matanka da kuma kome da yake naka, da bugu mai ƙarfi.
15
Kai kuma za ka kamu da ciwon hanji wanda zai yi ta cinka kowace rana sai har hanjinka sun fito.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options