2 Tarihi 14:1-5
1
Abiya kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki, a zamaninsa kuma ƙasar ta zauna lafiya na shekara goma.
2
Asa ya yi abin da yake da kyau da kuma daidai a gaban Ubangiji Allahnsa.
3
Ya kawar da baƙin bagade da masujadai bisa tudu, ya farfashe keɓaɓɓun duwatsu, ya kuma sassare ginshiƙan Ashera.
4
Ya umarci Yahuda su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, su kuma yi biyayya da dokoki da kuma umarnansa.
5
Ya kawar da masujadan kan tudu da bagadan turare a kowane gari a Yahuda, masarautar kuwa ta zauna lafiya a ƙarƙashinsa.
Settings