Skip to content
1 Timoti 4:6-10

1 Timoti 4:6-10

6
In ka nuna wa ’yan’uwa waɗannan abubuwa, za ka zama mai hidima mai kyau na Kiristi Yesu, wanda aka goya cikin gaskiyar bangaskiya da kuma koyarwa mai kyau wadda ka bi.
7
Ka kiyaye kanka daga tatsuniyoyi na rashin tsoron Allah da labaru banza na tsofaffin mata; a maimako, ka hori kanka ga zama mai tsoron Allah.
8
Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa.
9
Wannan magana tabbatacciya ce wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa.
10
Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options