Skip to content
1 Sama’ila 21:1-7

1 Sama’ila 21:1-7

1
Dawuda ya tafi Nob a wurin Ahimelek firist. Da Ahimelek ya gan shi sai ya firgita ya ce, “Me ya sa kai kaɗai ne? Me ya sa ba wani tare da kai?”
2
Dawuda ya ce wa Ahimelek firist, “Na zo aikin sarki ne, ya kuwa ce kada in sanar wa kowa abin da ya sa in yi. Na faɗa wa mutanena inda za su same ni.
3
Yanzu, me kake da shi a hannu? Ka ba ni burodi guda biyar, ko wani abu da kake da shi a nan.”
4
Amma firist ya ce wa Dawuda, “Ba ni da burodi iri na kowa da kowa, sai dai akwai burodin da aka tsarkake. Za ka iya ɗauka ku ci idan mutanenka ba su kwana da mata ba.”
5
Dawuda ya ce, “Lalle ne a keɓe muke daga mata. Mutanena sukan keɓe kansu a koyaushe suka tashi ’yar tafiya, balle fa a yau!”
6
Don haka firist ya ba shi keɓaɓɓen burodi, tun da yake babu wani burodi a can sai dai burodin Kasancewa da aka cire daga gaban Ubangiji, aka sa burodi mai zafi a maimakon wanda aka cire a ranar.
7
A ranar kuwa, ɗaya daga cikin bayin Shawulu yana can, a tsare a gaban Ubangiji, sunansa Doyeg, mutumin Edom, shugaban makiyayan Shawulu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options