Skip to content
1 Bitrus 1:1-2

Gaisuwa da Sallama

1 Bitrus 1:1-2
1
Bitrus, manzon Yesu Kiristi, Zuwa ga zaɓaɓɓu na Allah, baƙi a duniya, da suke a warwatse ko’ina a Fontus, Galatiya, Kaffadokiya, Asiya da kuma Bitiniya,
2
waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah Uba, ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu, don biyayya ga Yesu Kiristi, su kuma sami yayyafan jininsa. Alheri da salama su zama naku a yalwace.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 90 chars

Options