1 Sarakuna 21:17-29
17
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya mutumin Tishbe.
18
Ta ce, “Gangara don ka sadu da Ahab sarkin Isra’ila, wanda yake mulki a Samariya. Yanzu yana a gonar inabin Nabot, inda ya tafi yă mallake ta.
19
Ka ce masa, Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ba ka kashe mutum ka kuma ƙwace kayansa ba?’ Sa’an nan ka ce masa ga abin da Ubangiji ya ce, ‘A inda karnuka suka lashe jinin Nabot, karnuka za su lashe jininka, I, naka!’ ”
20
Ahab ya ce wa Iliya, “Wato, ka same ni kuma, abokin gābana!” Sai ya amsa ya ce, “Na same ka, domin ka sayar da kanka ga yin mugunta a gaban Ubangiji.
21
‘Zan kawo masifa a kanka. Zan kawar da zuriyarka, in kuma yanke daga Ahab kowane ɗa namiji na ƙarshe cikin Isra’ila, bawa ko ’yantacce.
22
Zan mai da gidanka kamar gida Yerobowam ɗan Nebat, da na Ba’asha ɗan Ahiya, domin ka tsokane ni har na yi fushi, ka kuma sa Isra’ila ya yi zunubi.’
23
“Game da Yezebel kuwa Ubangiji ya ce, ‘Karnuka za su cinye Yezebel a katangar Yezireyel.’
24
“Karnuka za su cinye waɗanda suke na Ahab waɗanda suka mutu a cikin birni, tsuntsayen sararin sama kuma za su cinye waɗanda suka mutu a jeji.”
25
(Babu wani mutum kamar Ahab, wanda ya ba da kansa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. Yezebel matarsa ce ta zuga shi.
26
Ya yi abar ƙyama ƙwarai ta wurin bin gumaka, kamar Amoriyawan da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ila.)
27
Sa’ad da Ahab ya ji waɗannan kalmomi, sai ya yage rigarsa, ya sa rigunan makoki, ya kuma yi azumi. Ya kwanta a kayan makoki, ya kuma yi tafiya cikin sauƙinkai.
28
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya mutumin Tishbe, ta ce,
29
“Ka lura da yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana kuwa? Domin ya ƙasƙantar da kansa, ba zan kawo wannan masifa a kwanakinsa ba, amma zan kawo ta a kan gidansa a kwanakin ɗansa.”
Settings