Skip to content
1 Sarakuna 20:22-28

1 Sarakuna 20:22-28

22
Daga baya, annabin ya zo wurin sarkin Isra’ila ya ce, “Ka ƙarfafa matsayinka ka kuma ga abin da za a yi, gama a bazara mai zuwa sarkin Aram zai sāke kawo yaƙi.”
23
Ana cikin haka, shugabannin sarkin Aram suka ba shi shawara, “Allolinsu, allolin tuddai ne. Shi ya sa suka fi mu ƙarfi. Amma in mun yaƙe su a fili, tabbatacce za mu fi su ƙarfi.
24
Ka yi wannan. Ka cire dukan sarakuna daga matsayinsu ka sa waɗansu shugabanni a maimakonsu.
25
Dole kuma ka tā da waɗansu mayaƙa kamar waɗanda ka rasa, doki don doki, keken yaƙi kuma don keken yaƙi, saboda mu iya yaƙe Isra’ila a fili. Ta haka tabbatacce za mu fi ƙarfinsu.” Sai ya yarda da su, ya kuma yi haka.
26
Bazara na biye Ben-Hadad ya tattara Arameyawa, ya haura zuwa Afek don yă yaƙi Isra’ila.
27
Sa’ad da aka tattara Isra’ilawa, aka kuma ba su guzuri, sai suka taka suka fita don su sadu da Arameyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani ɗaura da su kamar ƙananan garkuna biyu na awaki, yayinda Arameyawa suka rufe dukan jejin.
28
Sai mutumin Allah ya zo ya ce wa sarkin Isra’ila, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Domin Arameyawa suna tsammani Ubangiji allahn tuddai ne, ba allahn kwari ba, zan ba da wannan ɗumbun mayaƙa a hannuwanka, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options