1 Sarakuna 2:13-17
13
To, sai Adoniya, ɗan Haggit ya tafi wurin Batsheba mahaifiyar Solomon. Ita kuwa ta tambaye shi ta ce, “Lafiya?” Ya amsa ya ce, “I, lafiya.”
14
Sa’an nan ya ƙara da cewa, “Ina da ɗan wani abin da zan faɗa miki.” Ta ce, “Faɗa.”
15
Sai ya ce, “Kamar yadda kika sani, mulkin nan nawa ne. Dukan Isra’ila suna ɗaukana a matsayin sarki. Amma abubuwa suka canja, sai mulkin ya koma ga ɗan’uwana; gama ya zo masa daga Ubangiji ne.
16
Yanzu ina da roƙo guda da zan yi gare ki. Kada ki hana mini.” Ta ce, “Sai ka faɗa.”
17
Sai ya ci gaba, “In kin yarda, ki yi magana da Sarki Solomon, gama ba zai ƙi jinki ba, ki ce yă ba ni yarinyan nan, Abishag, mutuniyar Shunam, tă zama matata.”
Settings