1 Sarakuna 18:19-24
19
Yanzu ka tara mutane daga dukan Isra’ila su sadu da ni a kan Dutsen Karmel. Ka kuma kawo annabawa ɗari huɗu da hamsin na Ba’al, da kuma annabawa ɗari huɗu na Ashera, waɗanda suke ci a teburin Yezebel.”
20
Sai Ahab ya aika a duk fāɗin Isra’ila, ya kuma tattara annabawan a kan Dutsen Karmel.
21
Iliya ya je gaban mutane ya ce, “Har yaushe za ku yi ta yawo tsakanin ra’ayoyi biyu? In Ubangiji ne Allah, ku bi shi; amma in Ba’al Allah ne, ku bi shi.” Mutane dai ba su ce uffam ba.
22
Sai Iliya ya ce musu, “Ni ne kaɗai annabin Ubangiji da ya rage, amma Ba’al yana da annabawa ɗari huɗu da hamsin.
23
Ku samo mana bijimai biyu. Bari su zaɓa ɗaya wa kansu, bari kuma su yanka shi kucu-kucu su sa a itace, sai dai, kada su sa wuta a kansa. Ni kuwa zan shirya ɗaya bijimin in sa a kan itace, ni ma, ba zan sa wuta a kansa ba.
24
Sa’an nan ku kira bisa sunan allahnku, ni kuwa zan kira bisa sunan Ubangiji. Duk allahn da ya amsa ta wurin wuta, shi ne Allah.” Sai dukan jama’a suka ce, “Abin nan da faɗa yana da kyau.”
Settings