1 Sarakuna 14:1-8
1
A lokacin Abiya, ɗan Yerobowam ya kamu da ciwo,
2
sai Yerobowam ya ce wa matarsa, “Ki tafi, ki ɓad da kama, don kada a gane ke a matsayin matar Yerobowam. Ki je Shilo. Annabi Ahiya yana a can, wannan wanda ya ce mini zan zama sarki a bisa wannan mutane.
3
Ki ɗauki dunƙulen burodi goma tare da ke, da waina, da tulun zuma, ki tafi wurinsa. Zai faɗa miki abin da zai faru da yaron.”
4
Saboda haka matar Yerobowam ta yi abin da ya faɗa, ta kuma tafi gidan Ahiya a Shilo. Yanzu dai Ahiya ba ya gani; idanunsa sun tafi saboda tsufa.
5
Amma Ubangiji ya ce wa Ahiya, “Matar Yerobowam tana zuwa tă tambaye ka game da ɗanta, gama yana ciwo, za ka kuwa ba ta amsa kaza da kaza. Sa’ad da ta iso za tă yi kamar wata ce dabam.”
6
Saboda haka sa’ad da Ahiya ya ji motsin sawunta a ƙofa, sai ya ce, “Ki shigo, matar Yerobowam. Me ya sa kike yi kamar wata ce dabam? An aiko ni wurinki da labari marar daɗi.
7
Je ki faɗa wa Yerobowam cewa ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na tā da kai daga cikin mutane, na mai da kai shugaba a bisa mutanena Isra’ila.
8
Na yage mulki daga gidan Dawuda na ba da shi gare ka, amma ba ka zama kamar bawana Dawuda wanda ya kiyaye umarnaina ya kuma bi ni da dukan zuciyarsa, yana yin abin da yake daidai kaɗai a idanuna ba.
Settings