1 Yohanna 4:1-6
1
Abokaina ƙaunatattu, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya.
2
Ga yadda za ku gane Ruhun Allah, duk ruhun da ya yarda cewa Yesu Kiristi ya zo cikin jiki, to, daga Allah yake.
3
Amma duk ruhun da bai yarda da Yesu ba, ba daga Allah ba ne, ruhun magabcin Kiristi ne, wanda kuka ji yana zuwa, har ma ya riga ya shigo duniya.
4
Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma.
5
Su daga duniya ne saboda haka suke magana yadda duniya take ganin abubuwa, duniya kuwa tana sauraronsu.
6
Mu daga Allah ne, kuma duk wanda ya san Allah yakan saurare mu. Amma duk wanda ba daga Allah ba, ba ya sauraronmu. Ta haka ne muke gane Ruhun gaskiya, da kuma ruhun ƙarya.
Settings