Skip to content
1 Korintiyawa 13:13

1 Korintiyawa 13:13

Ana nuna aya 13 tare da mahallin da ke kewaye.
10
Sai dai sa’ad da cikakken ya zo, sai wanda ba cikakke yă shuɗe.
11
Sa’ad da nake yaro, na yi magana kamar yaro, na yi tunani kamar yaro, na yanke shawara kamar yaro. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin yarantakata.
12
Yanzu kam muna ganin abubuwa kamar a madubi sai dai ba sosai ba, amma a ranan nan za mu gani fuska da fuska. Yanzu kam sanina ba cikakke ba ne, amma a ranan nan zan kasance da cikakken sani, kamar dai yadda Allah ya san ni a yanzu.
13
Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options