1 Tarihi 6:31-32
31
Waɗannan su ne mutanen da Dawuda ya sa su lura da waƙa a cikin gidan Ubangiji bayan da aka kawo akwatin alkawari yă huta a can.
32
Suka yi hidima da waƙa a gaban tabanakul, Tentin Sujada, sai da Solomon ya gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi ayyukansu bisa ga ƙa’idodin da aka shimfiɗa musu.
Settings