1 Tarihi 5:11-17
11
Mutanen Gad sun zauna kusa da mutanen Ruben a Bashan, har zuwa Saleka.
12
Yowel shi ne babba, sai Shafan na biyu, sa’an nan Yanai da Shafat, su ne tushen Bashan.
13
Danginsu, bisa ga iyalai su ne, Mika’ilu, Meshullam, Sheba, Yorai, Yakan, Ziya da Eber, su bakwai ne duka.
14
Waɗannan su ne ’ya’yan Abihayil ɗan Huri, ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Mika’ilu, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz.
15
Ahi ɗan Abiyel, ɗan Guni, shi ne kan iyalinsu.
16
Mutanen Gad sun zauna a Bashan da ƙauyukan da suke kurkusa da shi, da kuma a dukan makiyayan Sharon har zuwa iyaka inda suka kai.
17
Dukan waɗannan sun shiga tarihin zuriya a lokacin mulkin Yotam sarkin Yahuda da Yerobowam sarkin Isra’ila.
Settings