Skip to content
1 Tarihi 28:19

1 Tarihi 28:19

Ana nuna aya 19 tare da mahallin da ke kewaye.
16
yawan zinariya don kowane tebur saboda burodi mai tsaki; da kuma yawan azurfa saboda teburin azurfa;
17
yawan zinariya zalla, don cokula masu yatsu, kwanonin yayyafawa ruwa da kuma tuluna; yawan zinariya don kowane kwanon zinariya; yawan azurfa don kowane kwanon azurfa;
18
da kuma yawan tacecciyar zinariya don bagaden turare. Ya kuma ba shi tsari don keken yaƙi, wato, kerubobin zinariyar da suka miƙe fikafikansu suka inuwantar da akwatin alkawarin Ubangiji.
19
Dawuda ya ce, “Dukan wannan, ina da shi a rubuce daga hannun Ubangiji zuwa gare ni, ya kuma ba ni ganewa cikin dukan tsarin fasalin, filla-filla.”
20
Dawuda ya kuma ce wa Solomon ɗansa, “Ka yi ƙarfin hali, ka kuma yi aikin. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya, gama Ubangiji Allah, Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ko yă yashe ka ba, sai an gama dukan aikin saboda hidimar haikalin Ubangiji.
21
Sassan firistoci da na Lawiyawa suna a shirye domin dukan aiki a haikalin Allah, kuma kowane gwani mai niyya a kowace sana’a, zai taimake ka a cikin dukan aikin. Shugabanni da dukan mutane za su yi biyayya da kowane umarninka.”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 90 chars

Options