1 Tarihi 28:11-19
11
Sa’an nan Dawuda ya ba ɗansa Solomon tsari domin shirayin haikalin, gine-ginensa, ɗakunan ajiyarsa, ɓangarorin bisansa, ɗakunan cikinsa da kuma wurin kafara.
12
Ya ba shi tsarin dukan abin da Ruhu ya sa a zuciyarsa saboda filayen haikalin Ubangiji da ɗakunan kewaye, da ma’ajin haikalin Allah da kuma baitulmali na kayayyakin da aka keɓe.
13
Ya ba shi tsari game ɓangarori na firistoci da Lawiyawa, da game dukan aikin hidima a cikin haikalin Ubangiji, da kuma game da dukan kayayyakin da za a yi amfani da su a hidima.
14
Ya kimanta yawan zinariya don dukan kayayyakin zinariyar da za a yi amfani a kowane irin hidima, da yawan azurfa don dukan kayayyakin azurfan da za a yi amfani a kowace irin hidima.
15
Da yawan zinariya don wurin ajiye fitilan fitilu da fitilunsu, da yawan zinariyan da za a yi amfani don kowace fitila da wurin ajiye fitilanta; da kuma yawan azurfa don kowane wurin ajiye fitila da fitilunsa bisa ga yadda za a yi amfani da kowane wurin ajiye fitila;
16
yawan zinariya don kowane tebur saboda burodi mai tsaki; da kuma yawan azurfa saboda teburin azurfa;
17
yawan zinariya zalla, don cokula masu yatsu, kwanonin yayyafawa ruwa da kuma tuluna; yawan zinariya don kowane kwanon zinariya; yawan azurfa don kowane kwanon azurfa;
18
da kuma yawan tacecciyar zinariya don bagaden turare. Ya kuma ba shi tsari don keken yaƙi, wato, kerubobin zinariyar da suka miƙe fikafikansu suka inuwantar da akwatin alkawarin Ubangiji.
19
Dawuda ya ce, “Dukan wannan, ina da shi a rubuce daga hannun Ubangiji zuwa gare ni, ya kuma ba ni ganewa cikin dukan tsarin fasalin, filla-filla.”
Settings